Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, kan yawan ziyartar sansanonin ’yan gudun hijira a Najeriya, yana nuna shakku kan sahihancin tawali’un da yake nunawa.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wani bikin karrama wasu fitattun ’yan ƙabilar Idoma da aka gudanar a Abuja, inda ya gargaɗi ’yan Najeriya da su yi hattara da ’yan siyasar da ya zarga da yaudarar jama’a gabanin zaɓen 2027.
Ministan ya tambayi dalilin da ya sa Obi, wanda a cewarsa bai taɓa gudanar da bikin ranar haihuwarsa a sansanin ’yan gudun hijira ba lokacin da yake gwamnan Jihar Anambra, yake yawan ziyartar irin waɗannan sansanoni a yanzu da yake neman shugabancin ƙasa.
“’Yan siyasa suna iya yin ƙarya. Mutumin da bai yi bikin ranar haihuwarsa a sansanin ’yan gudun hijira ba lokacin da yake gwamna, yanzu yana son yin hakan yana neman zama shugaban ƙasa. Sai ku ce yana da tawali’u. Wane irin tawali’u ne wannan?” Wike ya tambaya.
A ranar 30 ga Satumba, Obi ya bayyana cewa ya ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira guda 12 a sassa daban-daban na Najeriya cikin ’yan makonnin baya-bayan nan. Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan inganta rayuwar mutanen da ke zaune a sansanonin.
Haka kuma, Wike ya soki wasu ’yan siyasa da yake zargi da nuna halin taimakon jama’a a bainar jama’a domin neman farin jini, ciki har da sayen gasasshen masara da gyada a kan hanya.
Ya buƙaci ’yan Najeriya da kada su bari irin waɗannan abubuwa su rinjayi ra’ayinsu game da ’yan siyasa, yana mai kare ƙoƙarin gwamnatin tarayya na magance matsalolin tattalin arziki da tsaro.
Ministan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su kwatanta halin da ƙasar ke ciki a yanzu da yadda take a baya, domin tantance ƙoƙarin da ake yi na inganta al’amura.
