Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) guda huɗu, da kwamishinonin zaɓe na jihohi guda biyu, sakamakon kammala wa’adin wasu jami’an hukumar.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 16 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta ce Tinubu ya sake naɗa Dakta Bala Bila, wanda ke wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.
Sauran sabbin kwamishinonin ƙasa sun haɗa da Farfesa Mustapha Aliu, wanda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru daga shiyyar Arewa maso Yamma, da Bashir Muhammed Umar, wanda zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu daga shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Haka kuma, shugaban ƙasar ya miƙa sunan kwamishinar zaɓe ta jihar Osun, Oluwatoyin Babalola, domin wakiltar shiyyar Kudu maso Yamma.
A ɓangaren kwamishinonin zaɓe na jihohi, Tinubu ya zaɓi Dakta Samuel Akinjide Akinleye domin wakiltar jihar Ekiti, yayin da Zahradden Basiru Sanusi zai wakilci jihar Jigawa, inda zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.
Shugaban ƙasar ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta gaggauta tantancewa tare da tabbatar da naɗin waɗanda aka zaɓa, yayin da ake shirin gudanar da babban zaɓen ƙasar da ake shirin gudanarwa a watan Janairun 2027.
