Gwamnatin Kano ta rantsar da sababbin masu baiwa Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara na musamman guda 21, tare da sake tabbatar da wasu mutum shida a muƙamansu.
Da yake jawabi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce waɗanda aka naɗa za su taimaka wa gwamnatinsa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryenta, tare da tabbatar da cewa ayyukan gwamnati sun kai ga amfanin al’ummar jihar.
Gwamnan ya buƙaci sabbin masu ba shi shawarar da su kasance masu kishin aiki, biyayya da jajircewa wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai da fahimtar juna tsakanin masu riƙe da muƙaman gwamnati, domin samun nasarar manufofin gwamnatin jihar da inganta rayuwar al’ummar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya ruwaito cewa an gudanar da bikin rantsar da sabbin masu ba gwamnan shawarar ne yayin taron Majalisar Zartarwar Jihar Kano karo na 41, da aka gudanar a Abuja.
