Wani sabon rahoto da cibiyar Famine Early Warning Systems Network (FEWS NET) ta fitar ya ce Akalla mutane kusan miliyan 16 ne a Najeriya za su ci gaba da fuskantar matsanancin karancin abinci nan da watan Janairun shekarar 2027.
Rahoton ya nuna cewa duk da ana sa ran girbin bana zai rage yawan masu fama da yunwa idan aka kwatanta da halin da ake ciki yanzu, matsalar za ta ci gaba da kasancewa mafi muni fiye da yadda ta kasance a shekarun baya.
Sai dai shugaban kungiyar manoma na kasa reshen jihar kano [AFAN] Abdullahi Ali Maibiredi yace duk da tsadar taki da ake fuskanta a yanzu amma suna sa ran noman bana zai wadaci yan Najeriya.
Rahoton FEWS NET ya kuma sanya Najeriya cikin ƙasashe huɗu da ke da mafi yawan mutanen da ke fama da yunwa a duniya,baya ga Sudan, Pakistan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.
