Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri da tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari.
Atiku ya yi wannan ganawa ta sirri da Yari ne, bayan ya karɓi baƙuncin tsohon gwamnan a gidansa da ke Abuja.
Bayan ganawar tasu, ba tare da shigar ’yan jarida ba, har yanzu ba a bayyana abin da suka tattauna ba.
Wannan na zuwa ne a yayin da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara ƙarfi a yayin da fitattun ’yan siyasa ke sauya sheƙa.
A kwanakin baya Atiku Abubakar ya sauya sheƙa daga Jam’iyyar PDP zuwa ADC, inda ake sa ran zai nemi takarar shugaban ƙasa domin sake ƙalubalantar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya kayar da shi a zaɓen 2023.
