‘Yansanda a jihar Kebbi sun ce sun kama wata mata mai shekara 19 a ƙaramar hukumar Zuru bisa zargin satar wani jariri da kuma gabatar da shi ga mijinta a matsayin ɗanta.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne bayan matar ta ziyarci mahaifiyar jaririn jim kaɗan bayan haihuwar yaron, inda ta yi alƙawarin kawo mata ruwan zafi amma ta tsere da jaririn.
Binciken farko ya nuna cewa wadda ake zargin ta yaudari mijinta na tsawon watanni tana mai nuna masa cewa tana da juna biyu. Daga bisani ta sace jaririn tare da kai shi gida tana cewa nata ne.
‘Yansanda sun ce an kama matar ne a ranar 14 ga Agustan 2026 bayan bincike, sannan an ceto jaririn tare da mayar da shi ga mahaifiyarsa.
Rundunar ta ce za a gurfanar da wadda ake zargin a kotu bayan kammala bincike
