
Kyautar Takalmin Zinare mai muhimmanci a kwallon kafa
Ƙyautar takalmin zinare da ake kira ‘European Golden Boot’, ana bayar da shi ne a duk ƙarshen kakar gasar kwallon kafa a Turai ga wanda ya fi kowa cin ƙwallaye a dukkannin kungiyoyin wasan kwallon na Turai.
An kuma kirkiri ƙyautar takalmin zinare ne a shekarar 1967 zuwa 1968, aka kuma sa masa sunan ƙyautar ‘Soulier d’Or’ – watau ‘Golden Shoe da Faransanci.
Jaridar Faransa ce L’Equipe ce ta fara gabatar da ƙyautar ta takalmin zinare tun daga kakar 1996-97.
Shin ko waye zai karbi kyautar mai tsohon tarihi a kwallon kafa a wannan shekarar?
Tun lokacin da aka kirkiri ƙyautar kusan shekara 60, kusan fitattun ƴan wasa ne ke lashe takalmin zinaren.
Ɗan wasan tawagar Portugal, Eusebio shi ne ya fara karɓar ƙyautar a 1968, bayan da ya zura ƙwallo 42 a Benfica, sai ya kara lashewa a mataki na biyu cikin kaka biyar.

Ian Rush shi ne ɗan Ingila na farko da ya lashe ƙyautar, sakamakon da ya ci ƙwallo 32 a Liverpool a kakar 1983/84
A kakar 1996/97 ɗan wasan Brazil, Ronaldo ya karɓi ƙyautar, kuma na farko a kasar da ya yi wannan bajintar.
Mai Ballon d’Or karo takwas, wato Lionel Messi ya ɗauki ƙyautar karo shida, shi kuwa abokin hamayyarsa, Cristiano Ronaldo ya lashe karo na huɗu.
A shekara 11 tsakani, Ronaldo da Messi suka fara mamaye ƙyautar, inda Ronaldo ya fara shiga tarihi a Manchester United a 2008, shi kuwa Messi ya fara ɗauka kaka biyu tsakani..
A karin wata kaka 11 tsakani ƴan wasan biyu sun lashe ƙyautar ta takalmin zinare karo takwas a tsakaninsu.
A kakar nan ana ganin sabon ɗan wasa ne zai lashe ƙyautar bana.
Ƙyaftin ɗin tawagar Ingila, Kane zai kawo ƙarshen wa’adinsa a ƴan kwanakin nan, bayan da ya ci ƙwallo 26 a bana a Bundesliga, kenan yana da maki 52 a matakin na huɗu a cikin ƴan takara.
Watakila za a samu sabon ɗan wasan da zai lashe ƙyautar bana a karon farko da ya haɗa da Viktor Gyokeres da Kylian Mbappe da kuma Mohamed Salah da ke ƴan ukun farko.
Ɗan ƙwallon Sporting, Gyokeres zai iya zama gwarzo a bana a matakin na farko ba daga cikin masu buga manyan gasar Turai biyar ba tun bayan 2002.
Ɗan wasan ya ci ƙwallo 39 a kakar nan, shi ne kan gaba da maki 58.5 a gasar tamaula ta Portugal – shi ya sa Arsenal ke zawarcin ɗan ƙwallon.
To sai dai ɗan wasan Sweden ya gama cin ƙwallaye, sakamakon da aka ƙare gasar Portugal – yayin da saura wasa ɗaya ya rage a gaban ɗan ƙwallon Real Madrid da na Liverpool, Salah da za su buga.
Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa yana da maki 58, zai iya haura Gyokeres da zarar ya ci ƙwallo a karawar da Real Madrid za ta karɓi bakuncin Real Sociedad ranar Asabar a La Liga.
Shi kuwa ɗan wasan tawagar Masar, Salah yana da maki 56, idan kuma yana son shan gaban Mbappe, yana bukatar zura ƙwallo biyu ko fiye da haka a raga.

Shin wa kuke gani zai ci kyautar a wannan karo?