‘Yan bindiga sun kai hari gidajen kwanan dalibai na kwalejin tarayya da ke Kaura Namoda a jihar Zamfara tare da sace dalibai su bakwai.
Wani daliban makarantar, Ibrahim Ahmad, ya bayyana cewa daya daga cikin daliban da aka sace ya yi nasarar tserewa, inda har yanzu dalibai uku maza da mata uku ke hannun ‘yan bindigar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren jiya, lokacin da ‘yan bindigar suka zo wucewa suka tarar da daya daga cikin gidan kwanan daliban a bude.
Ya kara da cewa daya daga cikin daliban ne ya fita waje domin ya huta, sannan ya bar kofar a bude ba da gangan ba, hakan bawa ‘yan bindiga damar shiga gidan tare da yin garkuwa da daliban.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa jami’an rundunar ‘yan sandan jihar (VCRU), tare da hadin gwiwar dakarun Operation Fansan Yamma, sun kaddamar da aikin ceto tare da hadin gwiwa, domin ganin an ceto daliban cikin gaggawa.
