Shugaban kungiyar Izala dake Legas kuma limamin massalacin Juma’a na 1004 Imam Sulaiman Ibrahim, ya ja hankulan al’umma musamman yan Arewa dasu harzarta domin sabunta rijistar zaben su.
Iman Sulaiman ya ce ta hakan ne kadai za’a iya magance duk wasu motsalolin da Kasar nan ke ciki, wajan sake zabar shugabanni nagari.
Imam Sulaiman ya bayyana haka ne a wani fefan bidiyon da ya aikowa Premier Radio, wanda ya ce rashin yin rijistar domin zaben shugabanci wani gibi ne a cikin al’umma.
Imam ya kuma ce a yanzu haka kudancin Najeriya na sahun gaba wajan sabunta katunan su, wanda hakan ke nuni da cewa al’ummar arewa sun gaza a wannan bangare.
Ya kuma kara da cewa, duk da suma sukan fuskanci kalubale wajan sabuta rijistar ta hanyar chanza musu mazabar da suke, amma hakan baisa sun bujure ba.
Masana da masu ruwa da tsaki dai na ci gaba da kira ga al’umma dasu fito ranar zabe, domin tantance shugabanci na gari.
