Tsohon kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya bai wa sabon kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wa’adin sa’o’i 48 domin ya janye wasu kalaman da ya yi a kansa, tare da neman afuwa a bainar jama’a, ko kuma ya fuskanci shari’a.
Mustapha, wanda ɗa ne ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kuma mataimakin ɗan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NDC, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Matakin nasa na zuwa ne bayan wani faifan bidiyo daga shirin talabijin mai suna Gabon Talk Show ya bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ji Sanusi Bature na magana kan zargin da ake yi wa Mustapha na mu’amala da miyagun ƙwayoyi.
A cikin faifan bidiyon, Sanusi Bature ya yi ikirarin cewa Sanata Kwankwaso ya kai ɗansa cibiyoyin gyaran ɗabi’a da dama domin ya daina mu’amala da miyagun ƙwayoyi, sannan ya nuna cewa mahaifinsa zai yi nadamar fitowarsa a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamna.
Sai dai Mustapha ya musanta waɗannan zarge-zarge, yana mai cewa ƙarya ne kuma an yi su ne domin ɓata masa suna.
Ya kuma musanta zargin cewa mahaifinsa ya riƙa kai shi cibiyoyin gyaran ɗabi’a a ƙasashe daban-daban, ko kuma cewa an kafa cibiyar gyaran ɗabi’a ta Kiru ne musamman saboda shi.
Game da cibiyar ta Kiru, Mustapha ya ce an kafa ta ne a lokacin wa’adin mulkin mahaifinsa na biyu a matsayin gwamnan Kano, lokacin da shi kuma yake zaune a Dubai.
Ya bayyana cewa cibiyar wani shiri ne na gwamnatin jihar domin gyara tarbiyyar matasa, taimaka musu su dawo cikin al’umma da kuma ba su damar sake gina rayuwarsu, yana mai cewa dubban matasa sun amfana da ayyukanta.
Haka kuma, Mustapha ya musanta zargin cewa mahaifinsa bai taɓa damƙa masa amanar kula da jami’o’in Skyline da Mewar ko gonarsa ba.
Ya ce mahaifinsa ya tarbiyyantar da shi ne domin ya zama mai dogaro da kai, ba wai ya dogara da dukiyarsa ba, yana mai cewa ya kafa kamfanoni da sana’o’i da dama da kansa, ciki har da masana’antar sarrafa shinkafa da ke samar da ayyukan yi a Kano.
Dangane da naɗinsa a matsayin kwamishinan matasa da wasanni a baya, Mustapha ya ce ba a naɗa shi ba ne domin a gyara halayensa, kamar yadda ya ce kalaman kwamishinan suka nuna, sai dai domin ya yi wa al’ummar Kano hidima, musamman matasa.
Ya kuma yi tambaya kan ko ofishin kwamishinan yaɗa labarai an ƙirƙire shi ne domin sanar da al’umma manufofi da ayyukan gwamnati, ko kuma domin kai hare-haren siyasa kan abokan hamayya.
A cikin sanarwar, Mustapha ya ce:
“Ta haka nake bai wa Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa wa’adin sa’o’i 48 daga ranar Talata domin ya janye kalaman da aka danganta masa, tare da neman afuwa a bainar jama’a gare ni, iyalina da kuma al’ummar jihar Kano.”
Ya yi gargaɗin cewa idan kwamishinan bai bi wannan umarni ba cikin wa’adin da ya bayar, lauyoyinsa za su ɗauki matakin shari’a.
Mustapha ya ce ba zai bari a yi amfani da siyasa wajen ɓata masa suna, na iyalinsa da kuma tarihin hidimar da ya yi wa al’umma ba.
Sai dai ya jaddada cewa ba ya son shiga musayar yawu, yana mai cewa ya kamata a mayar da muhawarar siyasa kan manufofi, shirye-shirye da ayyukan da ’yan siyasa suka gudanar, maimakon kai hare-hare kan rayuwarsu ta kashin kai.
