Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta tanadi gine-ginen masauki guda uku a yankin Masfala na birnin Makkah, domin saukar da maniyyata 3,529 daga jihar yayin aikin Hajjin 2027.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi, ya fitar.
Sanarwar ta ce Shugaban Hukumar, Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ya bayyana hakan yayin ziyarar duba masaukan da aka tanada a ƙasar Saudiyya.
Matawalle ya ce gine-ginen guda uku suna kusa da juna, a yankin da ba shi da nisa da Masallacin Harami.
Ya ƙara da cewa hukumar ta gana da shugabannin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da hukumomin Saudiyya domin tattauna shirye-shiryen aikin Hajjin 2027.
Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen samar da sauran hidimomin da za su sauƙaƙa wa maniyyatan Kano gudanar da ibadarsu.
