Mai Shari’a Dehinde Dipeolu ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan sauraron buƙatar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta gabatar ta hannun lauyanta, Hanatu Kofar naisa.
Hukumar EFCC ta nemi kotun ta mayar da umarnin wucin gadi na kwace wayoyin zuwa na dindindin, bisa tanade-tanaden dokar yaƙi da damfarar kuɗi da kuma Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Rahotanni sun nuna cewa wayoyin na da alaƙa da wani babban shirin damfarar intanet da hukumar ta bankado a watan Disambar 2024, a wani gini mai hawa bakwai da ke Victoria Island, Legas.
A yayin samamen da aka gudanar a lokacin, jami’an EFCC sun kama mutum 792, ciki har da ’yan Najeriya da kuma wasu ’yan ƙasashen waje, waɗanda ake zargi da gudanar da damfarar soyayya da kuma zuba jari ta intanet.
Hukumar ta ce wasu daga cikin waɗanda aka kama sun kasance suna horar da matasan Najeriya dabarun amfani da bayanan bogi wajen damfarar mutane a kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa.
