Hakimin Ɗambatta Sarkin Ban Kano, Dr. Mansur Muhtar, ya jagoranci buɗe masallaci a Kofar Gabas da ke garin Ɗambatta wanda marigayi Malam Mahmud Ɗambatta ya gina 1908 bayan kammala aikin sabunta ginin masallacin mai dimbin tarihi.
Barrister Abubakar Balarabe Mahmoud SAN, ne ya dauki nauyin sabunta masallacin tare da tabbatar da an kiyaye martaba da tarihin masallacin.
Da yake jawabi yayin bikin buɗe masallacin, Hakimin Ɗambatta, Dr. Mansur Muhtar, ya yaba da wannan gagarumin aiki, yana mai cewa sabunta guraren ibada musamman masu tarihi irin wannan na daga cikin abubuwan da ke ƙarfafa addini da haɗin kan al’umma.
Ya kuma yabawa Barrister AB Mahmud SAN bisa ɗaukar nauyin aikin bisa yadda ya tabbatar da ci gaba da adana tarihin magabata, tare da kula da wajen ibada.
Al’ummar da suka halarci taron da suka haɗa da Sa’in Kano Hakimin makoda, Sarkin Fulanin Ja’idanawa, Arc Aminu Dabo, Malam Abdurrahaman Umar Engr Lawan Audi da sauran al’ummar garin Ɗambatta da baki daga sassa daban-daban ne suka halarci taron buɗe masallacin, inda aka gudanar da addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya da ci gaban al’umma.
