Wata kotu a Las Vegas ta samu wani shugaban ƙungiyar ’yan daba ta South Side Compton Crips, Duane “Keffe D” Davis, da laifin kisan fitaccen mawakin rap Tupac Shakur, wanda aka kashe a shekarar 1996.
Alƙalan kotun 12 sun yanke hukuncin bai ɗaya, inda suka sami Davis da laifin kisan kai a matakin farko tare da amfani da makami wajen kisa.
Davis mai shekara 63, wanda ya musanta aikata laifin, na fuskantar yiwuwar hukuncin ɗaurin rai da rai ba tare da damar saki ba.
Bayan an karanta hukuncin, Davis ya shaida wa alƙalin cewa zai ɗaukaka ƙara. “Ina shirin ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci,” in ji Davis.
Hukuncin ya jawo jimami a kotun, bayan ’yar’uwar Tupac, Sekyiwa “Set” Shakur, ta fashe da kuka yayin da ake karanta hukuncin. Shi ma ɗan Davis ya rufe fuskarsa da hannu, yayin da wasu daga cikin mutanen da ke kotun ke share hawaye.
Masu gabatar da ƙara sun gina shari’ar ne kan kalaman da Davis ya yi a bainar jama’a tsawon shekaru, ciki har da bayanan da ya bayar cewa cikin littafin tarihinsa na shekarar 2019 da kuma faifan tattaunawarsa da masu bincike.
A cikin bayanan, Davis ya amince cewa yana cikin wata farar mota kirar Cadillac yayin da aka harbo harsasan da suka kashe Tupac daga cikinta. Ya kuma ce shi ne ya samar da bindigar da aka yi amfani da ita wajen kashe Tupac.
Masu gabatar da ƙara sun ce duk da sauye-sauyen da ke cikin bayanan Davis tsawon shekaru, akwai wani abu guda da bai canza ba, wato kasancewarsa cikin motar da aka yi harbin.
Babban mataimakin lauyan gwamnati, Binu Palal, ya ce idan masu yanke hukunci sun amince da bayanan Davis, ba lallai ba ne a nemi ƙarin hujjoji domin tabbatar da hannu a kisan.
Sai dai lauyoyin Davis sun ce kalamansa na baya sun samo asali ne daga “alfahari” da kuma ƙoƙarin tallata littafinsa da ƙara ɗaukaka sunansa. Sun kuma ce babu isassun wasu hujjoji da suka tabbatar da bayanan nasa.
sai da masu yanke hukuncin sun yi watsi da wannan hujja, masu gabatar da ƙara sun ce an kashe Tupac ne domin ramuwar gayya kan wani rikici da ya faru a wannan daren tsakanin tawagar mawakin da ɗan dan uwan Davis, mai suna Orlando “Baby Lane” Anderson.
A cewar hujjojin da aka gabatar a kotu, Tupac da wasu daga cikin tawagarsa sun yi wa Anderson duka a wani gidan caca da ke Las Vegas.
Daga bisani Davis ya ce fadan ya fusata shi, sannan ya shiga wata farar Cadillac tare da wasu mutum uku domin neman Tupac da shugaban kamfanin Death Row Records, Marion “Suge” Knight.
Ya ce ya miƙa bindiga zuwa kujerar baya na motar kafin su gano motar da Tupac da Knight suke ciki.
Masu gabatar da ƙara sun ce daga nan ne ɗaya daga cikin mutanen da ke kujerar baya ya buɗe wuta.
An harbi Tupac ne a ranar 7 ga Satumba, 1996, yayin da yake tsaye a jan wuta a wata hanya a Las Vegas. Farar Cadillac ta zo kusa da motarsa, sannan aka fara harbe-harbe.
An harbi mawakin sau da dama, kuma ya rasu sakamakon raunukan bayan kwanaki shida, yana da shekara 25.
Ko da yake masu gabatar da ƙara sun zargi Davis da shirya harin, har yanzu ba su gano hakikanin mutumin da ya harba harsasan da suka kashe Tupac ba. Sauran mutum uku da suke cikin Cadillac a lokacin harin duk sun riga sun rasu.
