Saurari premier Radio
22.5 C
Kano
Saturday, September 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciShugaba Bola Tinubu ya sauka a kasar China

Shugaba Bola Tinubu ya sauka a kasar China

Date:

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a birnin Beijing din kasar China, a wata ziyarar aiki da zai gudanar a kasar.

Tinubu ya sauka a kasar ne da safiyar wannan rana ta Lahadi, jim kadan bayan ya bar kasar nan shida tawagarsa tun a ranar Alhamis.

Da yake yiwa manema Labaran fadar shugaban kasa karin bayani, mai magana da yawun shugaba Tinubu Ajuri Ngelale, yace Tinubu zai gana da masu ruwa da tsaki na kasar, a yunkurin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Haka zalika ya kuma ce shugaba Tinubu zai tattauna da shugaban kasar China Xi Jinping, kan batutuwan da shuka shafi noma, fasahar sadarwa zuba jari da sauransu.

Ana kuma saran Tinubu, zai halarci taron tattaunawa kan batun kasashen da ke da alaka da kasar China daga nahiyar Afrika wato (FOCAC).

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...