Donald Trump ya ce mallakar tsibirin Greenland yana da matuƙar muhimmanci ga ƙirƙirar garkuwar tsaronsa ta Golden Dome.
Da yake magana a taron tattalin arzikin duniya a Davos, ya ce,
A shekarar da ta gabata, Trump ya ce garkuwar za ta fara aiki gadan-gadan kafin ƙarshen wa’adinsa na shugaban ƙasa a shekarar 2029.
Bayan fitar da kasafin kuɗin farko na dala biliyan 23, shugaban ya ƙiyasta kuɗin da za a kashe kan shirin a dala biliyan 175, amma ofishin kasafin kuɗi na majalisar dokokin ƙasar ya ce kuɗin da shirin zai laƙume na iya ninka wannan adadin har ninki biyar a cikin shekaru ashirin.
Tsare-tsaren sun ƙunshi hanyar sadarwa ta fasahar zamani a cikin ƙasa, da teku da sararin samaniya – musamman ma na’urori da za a kafa a sararin samaniya waɗanda za su iya daƙile makamai masu linzami.
