Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Cycling Africa sun sanar da gudanar da gasar tseren kekuna karo na biyu, wadda za a yi ranar 12 ga Disamba, 2026, a birnin Kano.
Gasar ta bana za a gudanar da ita ne ƙarƙashin taken “Ruwa Rayuwa Ne”, domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin samun tsaftataccen ruwa, kiyaye albarkatun ruwa da kuma sauyin yanayi.
A gasar farko da aka gudanar a shekarar 2025, an samu halartar sama da masu tseren kekuna da masoya wasanni dubu ɗaya daga sassan Najeriya.
Shugaban ƙungiyar Cycling Africa, Bamidele Adeleye, ya bayyana cewa nasarar gasar farko ta samu ne sakamakon goyon bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce yana amfani da wasanni wajen jawo hankalin matasa, bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
