Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, bisa zarginsa da gaza magance matsalar zaizayar ƙasa a lokacin da yake gwamnan Jihar Anambra.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin taron jam’iyyar APC da aka gudanar a birnin Uyo, Jihar Akwa Ibom.
Shugaban ƙasar ya ce a lokacin da yake gwamnan Legas, ya ɗauki matakan da suka taimaka wajen magance barazanar mamayar Tekun Atlantika, sabanin yadda ya zargi Obi da kasa tunkarar matsalar zaizayar ƙasa a Anambra.
Daga bisani, Tinubu ya ƙaddamar da wurin shakatawa na ARISE Palm Resort a Uyo, tare da yaba wa Gwamna Umo Eno bisa ayyukan samar da ababen more rayuwa a jihar.
