
Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ce yankin Arewa maso Yamma ne ke da mafi yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya yayin da ƙasar ke shirin shiga zaɓen shekarar 2027.
Jimillar masu rajistar zaɓe da hukumar ta bayyana ta kai sama da miliyan ɗari da uku bayan kammala aikin sabunta rajista da tsaftace bayanan masu zaɓe.
Kano ce ke da kusan miliyan 6.5, yayin da Kaduna ke da kusan miliyan 4.6, Katsina kuma kusan miliyan 3.8.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta shiga matakin ƙarshe na shirye-shiryen zaɓen, yayin da ya rage kwanaki ɗari kafin fara babban aikin zaɓe.
Hukumar ta ce tana fuskantar wasu ƙalubale da suka haɗa da tsaro, kuɗaɗen gudanar da zaɓe, sayen ƙuri’u da yaɗa bayanan ƙarya.
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ma ta ce tana ci gaba da matakan tsaro domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana.
