Screenshot
Gwamnatin Kano ta ce ta na baiwa tattara sahihan bayanai da ƙididdiga muhimmiyar kulawa wajen tsara manufofi da shirye-shiryen gwamnati.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da yake buɗe taron kwamitin tuntuɓa na ƙasa kan ƙididdiga karo na farko da ake gudanarwa duk bayan watanni shida a Kano.
Gwamnan, wanda sakataren gwamnatin kano Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya wakilta, ya ce ƙididdiga muhimmin ginshiƙi ne wajen tafiyar da gwamnati cikin inganci da tsara shirye-shiryen da suka dace da buƙatun al’umma.
Tun da farko, shugaban hukumar ƙididdiga ta Ƙasa, Prince Adeyemi Adeniran, ya ayyana sahihan bayanai da ƙididdiga a matsayin muhimman dabaru wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Prince Adeyemi na cewa tafiyar da gwamnati bisa sahihan bayanai na taimakawa wajen yanke hukunci mai kyau da kuma tsara shirye-shiryen gwamnati cikin inganci.
