Rundunar ta ce lamarin ya fara ne bayan wanda abin ya shafa, Metu Jilani, ya kai rahoto ga ’yan sanda a ranar 19 ga Satumba, inda ya bayyana cewa wasu mutane sun kira shi ta waya suna barazanar sace shi da iyalinsa.
A cewar rundunar, wadanda suka yi barazanar sun bukaci a tura musu naira miliyan uku zuwa asusun wani mai sana’ar POS mai suna Muhydeen Salihu da ke jihar Kwara, sai dai Jilani ya tura musu naira dubu 100 kacal, lamarin da ya taimaka wa jami’an tsaro wajen bincike.
Rundunar ta ce a ranar 18 ga Satumba, wasu mutane biyu, Hantsi Abdullahi da Hantsi Liman, sun je wajen ma’aikacin POS domin karɓar kudin, an kama Abdullahi yayin da Liman ya tsere, amma kafin jami’an ’yan sanda su kai shi asibiti, wasu fusatattun mutane sun yi masa dukan tsiya.
A yanzu dai Abdullahi yana kwance a asibiti, yayin da ’yan sanda ke ci gaba da neman abokin tafiyarsa da sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a lamarin.
Tuni dai kwamishinan ’yan sandan jihar Oyo ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike tare da gano duk wadanda ke da hannu a barazanar.
