Shugaban mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya sauke babban hafsan sojin ƙasar, Manjo Janar Moussa Salaou Barmou, tare da maye gurbinsa da Birgediya Janar Mahaman Sani Kiaou, wanda shi ne babban hafsan rundunar sojojin ƙasa a halin yanzu.
Ma’aikatar Tsaron ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, tana mai cewa matakin ya zo ne bisa wata doka da shugaban ƙasar ya zartar.
Sanarwar dai ba ta bayar da wani bayani kan dalilin cire Barmou daga muƙaminsa ba, duk da cewa yana riƙe da matsayin tun bayan karɓar mulki.
Korarsa daga muƙamin na daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi a rundunar sojin Nijar tun bayan juyin mulkin da ya kai Tchiani kan karagar mulki, kamar yadda sanarwa ta bayyana.
Hakan ya kuma biyo bayan yunƙurin juyin mulkin da aka ruwaito ya faru a ƙasar a ranar 29 ga Agustan da ya gabata.
