Hukumar Kula da lafiya a matakin farko ta Kano ta gudanar da taron kwanaki biyu, domin yin nazarin inganta tsarin gudanar da kuɗaɗe da bayar da rahotanninsu da nufin ƙara inganta gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati a cibiyoyin lafiya.
Taron wanda ya gudana a Zariya ta jihar Kaduna, ya mayar da hankali wajen duba tsarin da ake amfani da shi domin ya dace da sabbin dokokin gudanar da kuɗaɗen gwamnati da kuma ƙa’idojin kula da kuɗaɗen tallafin kiwon lafiya.
Da yake yiwa Premier radio karin bayani, Shugaban Hukumar Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya ce kyakkyawan tsarin tafiyar da kuɗaɗe shi ne ginshiƙin ingantaccen tsarin kiwon lafiya, yana mai cewa dole ne a inganta hanyar kashe kuɗin gwamnati ta yadda zai amfani al’umma.
Farfesa Salisu ya ce mahalarta taron sun amince da sabunta tsarin gudanar da kuɗaɗe, tare da fayyace rawar da masu ruwa da tsaki za su taka a fannonin kasafin kuɗi, saye da sayarwa, kashe kuɗi, rubuta rahotanni, adana bayanai da kula da kadarori.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Babban Sakataren ma’aikatar lafiya ta Kano, Pharmacist Aminu Bashir, na cewa ingantaccen tsarin kula da kuɗaɗe yana taimakawa wajen dorewar zuba jari a fannin lafiya.
