Sanata Francis Fadahunsi, mai wakiltar mazabar Osun ta Gabas, ya bukaci magoya bayansa da su sanya ido kan yadda mutane ke kada kuri’a a zaben gwamnan jihar Osun da ake gudanarwa a yau Asabar.
Sanatan na jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne a wata rumfar zabe da ke makarantar firamare ta NUD, a Ilase-Ijesa, cikin karamar hukumar Ilesa.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook, an ga sanatan yana magana da harshen Yarbanci, inda yake umartar magoya bayansa da su lura da yadda kowane mai kada kuri’a ya kada kuri’arsa.
Ya kuma ce duk wanda bai zabi jam’iyyar da ya kira “jam’iyyar da ta dace” a Ilesa ba, ba dan asalin Ilesa ba ne.
Wannan furuci na zuwa ne kwanaki uku bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta gayyaci sanatan domin yi masa tambayoyi kan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.
Cikin bidiyon, an ji Sanatan yana amfani da kalmar “a kashe” yayin da yake magana kan ‘yan jam’iyyar Accord, wadda gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ke takara a karkashinta.
Sai dai daga baya sanatan ya ce an dauki kalamansa ba daidai ba, yana mai cewa abin da yake nufi shi ne a “kashe Accord da kuri’u”, ba wai a yi amfani da tashin hankali ba.
‘Yan sandan sun ce sun gayyace shi ne domin binciken zargin cewa kalaman nasa na iya zama barazana, tunzura jama’a ko kuma tsoratar da masu zabe.
