Jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba shi da tabbacin Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ba zai ci amanarsa ba kamar yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka yi a cewarsa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai, inda ya ce a siyasance babu wanda zai iya tabbatar da cikakkiyar biyayya daga wanda ya ɗora a kan wani matsayi, duk kuwa da irin amana da goyon bayan da aka nuna masa.
Sai dai jagoran Kwankwasiyyar ya jaddada cewa ya zaɓi Gwarzo ne bisa la’akari da ƙwarewa, jajircewa da kuma irin gudunmawar da ya bayar a tafiyar siyasar Kano da Kwankwasiyya.
Kwankwaso ya ce tarihi ya nuna yadda wasu daga cikin waɗanda ya marawa baya a baya suka sauya akala bayan sun samu mulki, lamarin da ya sa ba zai iya bayar da tabbacin abin da zai faru nan gaba ba.
