Zaman Majalisar Wakilai na yau Talata ya rikice bayan ‘yan majalisar sun samu saɓani kan ƙudirin da ke neman soke amincewar da akai wa kudirin gyaran dokar zaɓe.
A yayin zaman majalisar, shugaban kwamitin dokoki da harkokin kasuwanci na majalisar, Francis Waive, ya gabatar da ƙudirin neman majalisar ta janye matsayinta na amincewa da kudurin da akayi a ranar 23 ga Disamba, 2025.
Lokacin da Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya nemi gabatar da ƙuri’ar ra’ayin yan majaliasar, masu adawa da shi ta fi ƙarfi fiye da ta masu goyon baya.
Sai dai duk da haka, kakakin ya yanke hukuncin cewa masu goyon baya ne suka fi rinjaye.
Hakan ya haifar da zanga-zanga a cikin zauren majalisar, inda wasu ‘yan majalisa suka fara nuna rashin amincewarsu da hukuncin da aka yanke.
- Majalisar wakilai ta sanya ranar ƙada kuri’a kan kudirin kirkirar sabbin jihohi
- A sake tsarin zaben shugaban INEC – Gamayyar Jam’iyyun Siyasa
- Za Mu Kawar Da APC A Mulki A Zaben 2027 – Atiku Abubakar
Daga nan sai kakakin ya nemi a shiga zaman sirri (executive session), amma ‘yan majalisar suka ƙi amincewa da wannan shawara.
Duk da adawar da aka nuna, kakakin ya jagoranci majalisar zuwa zaman sirri.
A baya, lokacin da majalisar ta amince da gyaran dokar zaɓe a watan Disamba, ta kuma amince da tanadin da ke wajabta tura sakamakon zaɓen kai tsaye zuwa shafin duba sakamako na Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (IReV) domin tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓe.
