Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce manufar Kano First Agenda an ƙirƙire ta ne domin bai wa al’ummar jihar damar amfani da albarkatun cikin gida, ƙara musu ƙima da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin tallafawa mahauta 1,900 masu rijista, wanda Hukumar Kula da Ƙananan Sana’o’i da Masu Sana’ar tallace-tallace a Kan tituna Kano ta shirya.
Gwamna Abba ya ce manufar Kano First Agenda ta mayar da hankali ne kan bunƙasa sana’o’i, ƙara ƙimar albarkatun cikin gida da kuma tabbatar da cewa ci gaban tattalin arziki ya amfani kowane ɗan jihar.
Gwamna Abba ya ce manufar ta yi daidai da shirin gwamnatin tarayya na ƙarfafa amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin Najeriya, domin haɓaka samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnab na bayyana cewa an zaɓi mahautan da suka amfana da tallafin ne bayan tuntuba da shugabannin ƙungiyoyinsu, domin faɗaɗa kasuwancinsu da inganta rayuwar mambobinta.
