Aƙalla mutane 25 ne suka mutu, yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon wani rikici tsakanin al’ummomi biyu a kudu maso yammacin ƙasar Chadi.
Ma’aikatar Kula da Yankuna ta ƙasar ta bayyana cewa rikicin ya ɓarke ne a yankin Koula, bayan wata takaddama da ta taso lokacin da wani makiyayi ya kai shanunsa wurin shayar da dabbobi.
Rikicin ya rikide zuwa faɗa tsakanin al’ummomi biyu maƙwabta a yankin da ke kan iyakar lardunan Hadjer-Lamis da Bahr El-Ghazal.
Hukumomin Chadi sun bayyana cewa an kama mutane 39 da ake zargi da hannu a rikicin, tare da kai su birnin N’Djamena domin ci gaba da matakan shari’a.
A ranar Asabar, wata tawagar gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jagorancin ministoci da dama ta ziyarci yankin domin ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya da hana rikicin sake ɓarkewa.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa tana ƙarfafa tattaunawa tsakanin al’ummomin da abin ya shafa domin samar da sulhu mai ɗorewa.
Chadi na daga cikin ƙasashen Afirka da ke fama da tasirin sauyin yanayi, inda takaddama kan filaye, wuraren kiwo da samun ruwa ke yawan haifar da rikici tsakanin manoma da makiyaya.
