Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da wasu sabbin hanyoyi masu tsawon kilomita 10 da gwamnatin jihar ta kammala ginawa a ƙananan hukumomin Sumaila da Wudil.
Da yake ƙaddamar da hanyoyin, Gwamna Abba ya ce hanyoyin, waɗanda kowace daga cikin ƙananan hukumomin biyu suka samu kilomita biyar- biyar na daga cikin manufar gwamnatin sa na inganta hanyoyi da sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin birane da ƙauyuka.
Gwamna Abba ya ce an aiwatar da ayyukan ne domin magance matsalolin ababen more rayuwa da kauyuka ke fuskanta a matakin ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arziƙin al’umma.
A cewar gwamnan fitilun da aka sanya a kan hanyoyin za su taimaka wajen ƙara tsaro tare da bai wa ’yan kasuwa damar ci gaba da gudanar da harkokinsu har bayan faɗuwar rana.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na buƙatar al’ummar yankunan da suka ci gajiyar ayyukan da su kula da hanyoyin da fitilun, yayin da mazauna Sumaila da Wudil suka nuna godiyarsu kan ayyukan.
