Jami’ar Bayero da ke Kano za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa domin tattauna manyan ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya da sauran ƙasashen Afirka, musamman ta fuskar tsaro, tattalin arziki, shugabanci da sauyin yanayi.
Taron, wanda shi ne karo na biyar, za a gudanar da shi ne ƙarƙashin Tsangayar Kimiyyar Tattalin Arziki da Gudanarwa ta jami’ar.
Da yake jawabi ga manema labarai, Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Farfesa Kabir Tahir Hamid, ya bayyana cewa rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, gurɓacewar muhalli da raunin hukumomi na daga cikin manyan batutuwan da masana za su tattauna.
Farfesan ya ce manufar taron ita ce haɗa masana da masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin magance waɗannan matsaloli, tare da samar da shawarwarin da za su taimaka wajen bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a nahiyar Afirka.
Za a gudanar da taron daga ranar Litinin zuwa Alhamis a sabon harabar Jami’ar Bayero, Kano.
Ana sa ran taron zai samu halartar masana daga ciki da wajen Najeriya, jami’an gwamnati, ƴan kasuwa da masu tsara manufofi, waɗanda za su gabatar da maƙaloli kan batutuwan da suka shafi ci gaban nahiyar.
Masu shirya taron na fatan shawarwarin da za a samar za su taimaka wajen inganta shugabanci, ƙarfafa tattalin arziki da samar da hanyoyin magance matsalolin tsaro a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
