Jam’iyyar PDP ta ce ta kafa kwamatoci na riƙon ƙwarya da za su kula da shugaancin jam’iyyar a jihohin Enugu da Delta da kuma Rivers dake yankin kudancin ƙasar nan.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’iyyar ta fitar a jiya juma’a, ta ce kwamatin gudanarwa ne ya amince da kwamatocin riƙon kwaryar ne bisa tanadin sashen doka na 29(2) na tsarin mulkin jam’iyyar ta PDP na shekarar 2025 da aka yi wa kwaskarima.
- PDP Ta Nuna Takaici Kan Ficewar Gwamna Fubara Zuwa APC
- Sabon shugaban PDP ya roki Sule Lamido ya bada hadin kai domin gyara jam’iyyar
- PDP Ta Zabi Sabon Shugaba A Ibadan
Zaɓukan shugabanci a jihohin kudu maso kudu na cikin abubuwan da suka ƙara jawo ruɗani a cikin jam’iyar, inda ɓangaren Ministan babban birnin Abuja Nyesom Wike ke zargin an yi wa waɗanda suke goya wa baya ƙarfa-ƙarfa bayan sun ci zaɓen ta hanyar soke shi.
Kwamatocin za su ɗauki ragamar jagorancin shugabancin jam’iyyar a jihohinsu na tsawon abin da bai wuce kwana 90 ba.
A watan Nuwambar data gabata ne aka zaɓi sababbin shugabannin jam’iyyar na ƙasa, wadda a yanzu haka Kabiru Tanimu Turaki SAN ke jagoranta jami’iyyar ta PDP a matsayin shugaban ta na kasa.
