Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin tallafawa hukumar bayar da agajin shari’a ta Najeriya kuɗi Naira miliyan 100 da sabuwar motar aiki, domin ƙarfafa ayyukanta da faɗaɗa damar da talakawa da masu rauni ke samu wajen kare haƙƙoƙinsu a kotu.
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar, mai shari’a Sulaiman Durosinlorun Kawu, tare da sauran jami’an hukumar.
Gwamnan ya jaddada cewa talauci bai kamata ya hana kowane ɗan Najeriya samun haƙƙin shari’a ba, kuma bai kamata a bar mutum a gidan gyaran hali ba tare da wakilcin lauya ba saboda rashin kuɗin biyan sa,
Ya kuma umarci kwamishinan shari’a da na ayyuka da su duba ofishin hukumar domin inganta gine-gine, samar da kayan aiki da gyara matsalar wutar lantarki, tare da buƙatar hukumomin da ke ɓangaren shari’a da su baiwa hukumar haɗin kai, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da zaman lafiya da goyon bayan gudanar da zaɓukan 2027 cikin gaskiya da lumana.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin gudanarwar hukumar, Mai Shari’a Sulaiman Kawu, ya ce ziyarar na daga cikin rangadin aiki da hukumar ke yi a jihohin arewa maso yamma domin ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi da inganta ayyukan bayar da agajin shari’a.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Kawu na bayyana cewa tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023, hukumar ta taimakawa mutane kusan 2,500 a Kano, tare da taimakawa wajen sakin fursunoni kusan 20 ta hanyar biyan tarar da kotu ta yanke musu.
