
Aminu Abdullahi Ibrahim
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Ƙasa, UBEC, ta fara gudanar da horaswar kwanaki huɗu kan inganta hanyoyin koyarwa da sakamakon karatun ɗalibai.
Ana gudanar da horaswar ne a nan jihar Kano, tare da halartar wakilan jihohin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Manufar shirin ita ce bai wa jami’an ilimi dabaru da ƙwarewar da za su taimaka wajen inganta koyarwa da koyo, sannan su yaɗa ilimin ga malamai da sauran masu ruwa da tsaki a jihohinsu.
Da take bayyana taron, Sakatararriyar Hukumar UBEC, Dakta Aisha Garba, wadda Daraktan shiyyar Arewa maso Gabas, Alhaji Abdullahi Jarma, ya wakilta, ta ce horaswar za ta taimaka wajen koyar da dabarun da za su inganta yadda ɗalibai ke samun ilimi, fahimtarsa da kuma amfani da shi a makaranta da wajen makaranta.
Alhaji Jarma ya ce shirin zai kuma horas da daraktocin kula da harkokin karatu da sa ido da tantance ayyuka daga hukumomin SUBEB na jihohin da suka halarta, domin inganta yadda ake bibiyar samuwar da amfani da kayan koyarwa da na koyo.
Ya ƙara da cewa shirin ya ƙunshi tsarin bada lada, inda jihohin da suka nuna ƙwazo wajen cimma manufofin sakamakon karatu da aka amince da su za su samu yabo da lada a ƙarshen shirin.
A nasa jawabin, Manajan Shirin, Olumayowa Aleshil, ya ce manufar shirin ita ce inganta sakamakon karatun ɗalibai, ƙara yawan yaran da ke samun ingantaccen ilimin bai ɗaya, da kuma taimaka wa yaran da ba sa zuwa makaranta su koma aji.
Ya bayyana cewa za a riƙa horas da malamai akai-akai, tare da samar da littattafai da sauran kayan koyarwa domin inganta yadda ake gudanar da darussa.
Aleshil ya ce shirin na gudana ne ƙarƙashin shirin HOPE-EDU, wanda zai taimaka wa jihohi wajen tsara tsarin koyarwa, sa ido da tabbatar da samar da kayan karatu ga ɗalibai.
Ya jaddada muhimmancin samun goyon bayan gwamnatocin jihohi domin tabbatar da dorewar shirin, musamman wajen ci gaba da samar da kayan koyarwa da tallafin hukumomi bayan kammala shirin.
Horon na kwanaki huɗu ya haɗa jami’an ilimi daga shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, domin ƙarfafa ƙwarewarsu kan dabarun koyarwa, sa ido da tantance ayyuka, kula da kayan karatu da kuma tsarin bayar da lada bisa sakamakon koyo.
