Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a yau domin halartar babban taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da aka shirya a jihar.
Wani faifan bidiyo da Dada Olusegun, mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na zamani, ya wallafa a shafin X, ya nuna lokacin da jirgin shugaban ƙasar ya sauka a filin jirgin saman Maiduguri, inda jami’an gwamnati da na tsaro suka tarbe shi.
Bidiyon ya kuma nuna dimbin magoya bayan APC da suka fito domin tarbar shugaban ƙasar. An gan su suna rawa, suna ɗaga tutocin jam’iyyar tare da sanya riguna masu ɗauke da saƙonnin yaƙin neman zaɓe, ciki har da “Hope 2.0” da “Tinubu Go Again”.
Ziyarar na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar APC na tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda ake sa ran Shugaba Tinubu zai nemi zarcewa a wa’adi na biyu tare da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, wanda ya fito daga jihar Borno.
Gabanin taron, hukumomin tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na Maiduguri. An jibge jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci, tare da takaita zirga-zirga a wasu manyan tituna domin tabbatar da tsaron shugaban ƙasa da sauran mahalarta taron.
