Hukumar Tsaro ta NSCDC a jihar Kano ta ce ta gano wani wurin tace man dizal da ake zargin ana gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba a unguwar Panisau, ƙaramar hukumar Ungogo, tare da kama mutum biyar.
A wata sanarwa da kakakin hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar ranar Juma’a, 30 ga Oktoban 2026, hukumar ta ce waɗanda aka kama suna gudanar da harkokin mai da iskar gas ba tare da rajista da izinin da ya dace ba.
Sanarwar ta bayyana sunayensu da Ibrahim Bello, mai shekara 28; Musbahu Adam, 38; Rabiu Dahiru, 27; Haruna Kabiru, 26; da Sunusi Ahmad, 25.
Hukumar ta ce jami’ai daga sassan kare muhimman kadarori da ababen more rayuwa, kula da harkokin mai da iskar gas, rundunar ɗauke da makamai da kuma yaƙi da fasa bututun mai ne suka gudanar da samamen.
Ta ƙara da cewa an rufe wurin, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma tantance matakin shari’a da za a ɗauka.
NSCDC ta yi gargaɗin cewa tace mai ba bisa ƙa’ida ba na iya jefa lafiyar jama’a cikin haɗari, gurɓata muhalli da kuma yi wa tattalin arziki illa.
Kwamandan hukumar a Kano, Hassan Mohammed Agalama, ya kuma buƙaci jama’a su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai kan ayyukan da suke zargi a yankunansu.
