Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ƙaddamar da wani sabon tsarin tantance wayoyin hannu mai suna Device Checker, domin daƙile yaɗuwar wayoyin bogi da kuma taimakawa wajen hana amfani da wayoyin da aka sace.
Hukumar ta bayyana cewa tsarin zai bai wa masu amfani da wayoyin hannu damar bincika sahihancin wayoyin da suke son saya, musamman waɗanda aka shigo da su daga ƙasashen waje ko kuma wayoyin hannu na hannu-biyu.
A cewar NCC, tsarin yana amfani da lambar IMEI, wadda ke bambanta kowace waya, domin tantance ko na’urar ta samu amincewar hukumar kuma ta cika ƙa’idojin amfani da hanyoyin sadarwa na Najeriya.
Hukumar ta ce sabon tsarin zai kuma taimaka wajen gano wayoyin da aka yi wa jabun lambar IMEI, tare da ba da damar katse wayoyin da aka tabbatar an sace daga dukkan hanyoyin sadarwar Najeriya.
NCC ta bayyana cewa an fara aiwatar da tsarin ne tun ranar 7 ga Oktoban 2026, inda ta buƙaci masu sayen wayoyi su riƙa tantance su kafin biyan kuɗi.
Yadda za a tantance waya
Masu amfani da wayoyin hannu za su iya buga lambar *315# ko ziyartar shafin hukumar na www.ncc.gov.ng/devicechecker domin tantance wayoyinsu.
Haka kuma, ana iya gano lambar IMEI ta waya ta hanyar buga *#06#.
Sai dai hukumar ta jaddada cewa tsarin ba zai bai wa NCC damar karanta saƙonnin mutane, sauraron kiran wayarsu ko bibiyar inda suke ba, domin manufarsa ita ce tabbatar da sahihancin na’urorin sadarwa da kare masu amfani da su.
