Gwamnatin Kano ta ce ta ware fiye da naira biliyan ɗaya da rabi domin gudanar da auren zawarawa ga mutane dubu uku, da nufin sauƙaƙawa al’ummar jihar masu buƙatar aure tare da inganta tarbiyya a tsakanin al’umma.
Shugaban Hukumar Hisbah ta Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai, kan shirye-shiryen da hukumar ke yi dangane da shirin.
Sheikh Daurawa ya ce daga cikin sabbin dokokin da hukumar ta bijiro da su a wannan karo akwai hana duk wanda ke son sakin matarsa yin hakan kai tsaye ba tare da ya gabatar da ƙorafinsa gaban hukumar ba domin tantance dalilan rikicin ta hanyar yin amfani da amfani da malamai, masana harkokin zamantakewa wajen sasanta ma’auratan kafin a amince da duk wani matakin saki.
A cewar Daurawa, gwamnatin jihar na ɗaukar matakai daban-daban da za su taimaka wajen rage matsalolin zamantakewa, musamman waɗanda suka shafi mata marasa aure, zawarawa da marayu.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Daurawa na yin kira ga al’ummar jihar da su bada haɗin kai ga hukumar domin cimma manufofin shirin da kuma tabbatar da zaman lafiya da ɗorewar aure a tsakanin iyalai.
