Hukumar kula da ‘yan gudun hijira da ‘yan ci-rani da kuma mutanen da aka raba da muhallansu ta Najeriya NCFRMI, ta ce yanzu haka akwai mutanen da suka rugo zuwa Najeriya daga kasashe kusan arba’in da uku domin samun rayuwa mai sauki.
Kasashen dai sun hada da Kamaru da Jamhuriyyar Dimokuradiyar Kwango da Siriya da sauran su domin neman mafaka.
Hukumar ta ce mutanen sun zo Najeriya don samun mafaka ne sakamakon rikice-rike da ake fama da su a kasashen nasu.
Jami’in hukumar mai kula da shiyyar arewa ta tsakiyar, Basheer Yusuf, ya shaida wa BBC cewa ‘yan gudun hijira masu neman mafakar da suka zo daga wasu kasashen zuwa Najeriya sun kai 138, 154.
Ya ce, Akwai ire-iren wadannan mutanen masu neman mafaka da suka kai 32, 748 da suka gudo daga wasu kasashe da ke jira a ba su damar samun mafaka a Najeriya.
A Najeriya kanta a cewar hukumar ta NCFRMI, akwai mutum fiye da miliyan uku da rabi da aka raba da muhallansu.
