Majalisar dattijai za ta tantance sabon gwamnan bankin kasa da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Dr Olayemi Cardoso domin tabbatar da nagartar sa kafin sahale masa hawa kujerar gwamnan babban bankin.
Haka zalika mataimakan gwamnan 4 da shugban kasa ya nada, zasu bayyana gaban majalisar a yau Talata domin tantancewa, kafin su sami sahalewar jagorantar al’amuran bankin zuwa shekaru 5 nan gaba.
Dr Cordoso dai tsohon kwamishinan kasafi da tsare tsaren tattalin arziki ne lokacin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a jihar Lagos.
Majalisar dattijan zata dawo aiki bayan dogon hutun watanni biyu, da shirin tantance karin sabbin ministoci 2 da shugaban kasa ya aike mata, a ranar talata 3 ga watan oktoba mai kamawa.
Idan za a iya tunawa dai shugaba Tinubu ya nada Dr Jamila Ibrahim da Ayodele Olawande a matsayin ministoci yayin da majalisar ke hutu