
Matashin dan shekara 20 ana zargin ya hallakata ne da duka ta tabarya a cewar kakakin rudunar ‘yansandan jihar
Mai magana da yawun ƴansandan jihar, CSP Ahmed Wakili ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin
Yana mai cewa, lamarin ya faru ne ranar 24 ga watan Fabrairu a wata unguwa mai suna Abujan Kwata.
“Matashin mai suna Safiyanu Dalhatu ɗan shekara 20, ya yi amfani da taɓarya wajen lakaɗawa mahaifiyarsa duka har ta kai ga mutuwarta. in ji shi.
“Bayan samun rahoton abin da ya faru ne muka aika tawagar jami’ansu zuwa anguwar, inda suka ɗauki mahaifiyar matashin zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa a inda likita ya tabbatar da mutuwarta”. In ji shi.
Ya kuma ce, suna riƙe da matashin a halin yanzu da kuma taɓaryar da ya yi amfani da ita domin ci gaba da bincike za kuma su miƙa wanda ake zargin hannun kotu domin yanke masa hukunci da zaran sun kammala.