
Aminu Abdullahi Ibrahim
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar da ke neman ƙarfafa kariya ga masu bayar da bayanan sirri (whistleblowers), bayan ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.
Kudirin, wanda Sanata Neda Imasuen ya dauki nauyin gabatarwa, na da nufin sake fasalin dokar Public Complaints Commission (PCC), domin ƙarfafa ikon hukumar wajen bincike, inganta ayyukan gwamnati da kuma samar da cikakkiyar kariya ta doka ga masu fallasa cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka.
Sanata Imasuen, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ɗa’a, ka’idojin aiki da korafe-korafen jama’a, ya ce dokar da ake amfani da ita a yanzu ta tsufa, domin ta shafe fiye da shekaru 20 ba tare da sabuntawa ba, kuma ba ta dace da sauye-sauyen zamani da tsarin mulki na yanzu.
Ya bayyana cewa sabon kudirin zai bai wa Hukumar Korafe-korafen Jama’a damar gudanar da bincike cikin inganci, neman takardu da hujjoji, bayar da shawarwari, da kuma inganta gaskiya, riƙon amana da kyakkyawan shugabanci a cibiyoyin gwamnati.
A cewarsa, ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da kudirin ya ƙunsa shi ne samar da tsarin kariya ga masu bayar da bayanan sirri, domin mutane su samu ƙarfin guiwar bayyana bayanan da suka shafi cin hanci, rashin tsaro, cin zarafin ofis da sauran laifuffuka ba tare da fargabar tsangwama ko ramuwar gayya ba.
Sanatan ya ƙara da cewa idan aka amince da kudirin ya zama doka, zai ƙarfafa ‘yancin cin gashin kan Hukumar Korafe-korafen Jama’a, inganta adalci a harkokin gudanarwa, rage son rai a ayyukan gwamnati, da kuma dawo da amincewar jama’a ga cibiyoyin gwamnati.
Ya kuma bayyana cewa kudirin ya yi daidai da ƙa’idodin ƙasa da ƙasa, inda hukumomin Ombudsman masu zaman kansu ke taka muhimmiyar rawa wajen kare haƙƙin jama’a, inganta shugabanci nagari da kuma tabbatar da ingantaccen gudanar da ayyukan gwamnati.
