Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC a Najeriya ta bayyana shirinta na tura jami’anta masu ɗauke da makamai domin sa ido kan babban zaɓen shekarar 2027.
Daraktan wayar da kan jama’a na hukumar, Demola Bakare, ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen zaɓen 2027 da aka gudanar ta intanet a ranar Alhamis.
Bakare ya ce hukumar ta horas da wasu jami’anta kan amfani da makamai, waɗanda za a tura domin taimakawa wajen sa ido kan yadda za a gudanar da zaɓukan.
Ya bayyana cewa ya kamata a fara shirye-shiryen sa ido kan zaɓe tun watanni kafin ranar kaɗa ƙuri’a, domin bai wa jami’ai damar fahimtar dokokin zaɓe da na aikata laifuka.
A cewarsa, cin hanci da rashawa na iya yin tasiri kan sahihancin zaɓe, musamman ta hanyar sayen ƙuri’u, amfani da dukiyar gwamnati wajen siyasa, tsoratar da masu zaɓe da kuma sauya bayanan zaɓe ba bisa ƙa’ida ba.
Jami’in ya jaddada cewa hukunta waɗanda aka samu da aikata laifukan zaɓe zai taimaka wajen hana wasu aikata irin waɗannan laifuka.
Ya kuma buƙaci jami’an da ke sa ido kan zaɓe su kasance masu zaman kansu, ba tare da nuna goyon baya ga wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara ba.
Bakare ya ce dole ne masu sa ido su tattara sahihan hujjoji tare da kiyaye su yadda za a iya amfani da su a kotu idan buƙatar hakan ta taso.
An gudanar da taron ne ƙarƙashin shirin ƙarfafa hanyoyin gano, sa ido da bayar da rahoto kan cin hanci da rashawa a zaɓen 2027.
Ƙungiyar Praxis ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Cibiyar Bunƙasa Albarkatun Ɗan Adam ta Jami’ar Lagos.
