Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, musamman Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, wajen ɓata masa suna da kuma jawo shi cikin takaddamar siyasa.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar da sahihancinsa ranar Juma’a, inda ya bayyana damuwarsa kan lalacewar dangantakarsa da gwamnan, wadda ya ce ta daɗe tana tsakanin su tsawon shekaru 43.
Ya ce Abba Yusuf ya taɓa yi masa aiki a matsayi daban-daban, ciki har da mai taimaka masa na musamman (PA), babban sakataren ofishinsa (PPS) da kuma kwamishina.
A cewarsa, Abba Yusuf ne ɗan takarar da tafiyarsu ta siyasa ta tsayar a zaɓen gwamna na 2019 da 2023, inda ya samu nasara a zaɓen 2023 sakamakon haɗin gwiwarsu.
Kwankwaso ya ce an yi amfani da amincewar da ya bai wa Abba
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa tsawon shekarun da suka yi suna tare da amincewar da ya bai wa Abba Yusuf sun ba shi damar sanin irin muhimmancin da yake bai wa mutunci da amana.
Sai dai ya yi zargin cewa an yi amfani da wannan amincewa ta hanyar da ba ta dace ba.
Kwankwaso ya ce: ”Alakar da ta daɗe tana tsakaninmu tsawon shekaru 43 da kuma amincewar da na yi da shi, sun ba shi damar sanin bayanai da fahimtar irin muhimmancin da nake bai wa mutunci da amana, abin takaici, an yi amfani da wannan amincewa ta hanyar da ba ta dace ba.”
Ya kuma yi zargin cewa gwamnan yana ƙoƙarin jawo shi da iyalansa cikin ce-ce-ku-cen jama’a ta hanyar amfani da hukumomin gwamnati domin ɓata sunan da ya shafe kusan shekaru 50 yana ginawa.
Zargin amfani da EFCC da ƙungiyar SACGGI
Kwankwaso ya yi zargin cewa watanni da suka gabata Gwamna Abba Yusuf ya gabatar da buƙata a hukumance ga EFCC domin ta fara bincikarsa.
Ya ce bayan da wannan yunƙuri bai samu nasara ba, sai aka yi amfani da wata ƙungiya mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative (SACGGI).
Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa ƙungiyar ba ta da rajista a Hukumar Kula da Rijistar Kamfanoni ta CAC, kuma ba ta da sahihiyar kafar sadarwa ta zamani ko wata alaƙar hukuma da EFCC ko Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta ta ICPC.
Ya kuma zargi ƙungiyar da shirya zanga-zanga a harabar ofishin EFCC domin matsa wa hukumar lamba ta gudanar da bincike a kansa.
Rahotannin da aka wallafa a ranar 25 ga Nuwamba sun tabbatar da cewa ƙungiyar SACGGI ta gudanar da zanga-zanga a hedikwatar EFCC da ke Abuja, inda ta miƙa wa hukumar ƙorafi kan kadarorin da ake zargin suna da alaƙa da Kwankwaso.
Zargin amfani da INEC da ɓangaren shari’a
Kwankwaso ya kuma zargi Gwamna Abba Yusuf da wasu jami’an gwamnatinsa da amfani da kafafen yaɗa labarai wajen yaɗa bayanan da aka fitar a zaɓe, domin nuna shi a mummunar fuska da ɓata masa suna.
Ya danganta waɗannan matakai da shirye-shiryen babban zaɓen 2027, yana mai cewa suna iya zama wata dabara ta karkatar da hankalin jama’a, raunana ƙarfin siyasarsu da kuma kawo cikas ga shirinsu na shiga zaɓen.
Tsohon gwamnan ya kuma yi zargin cewa gwamnan na ƙoƙarin yin tasiri a wasu hukumomin gwamnati, ciki har da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ɓangaren shari’a.
A cewarsa, ana ƙoƙarin hana buga sunan ɗan takararsu na gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam, da kuma hana shi shiga zaɓen 2027, lamarin da ya ce zai iya ba gwamnan damar yin takara ba tare da abokin hamayya ba.
Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan matakai na iya ƙara zafin siyasa da sanya zaman lafiya da tsaron Kano cikin haɗari.
Ya yabawa EFCC kan yadda ta gudanar da gayyatar da ta yi masa
Duk da zargin da ya yi kan amfani da hukumar a rikicin siyasa, Kwankwaso ya yaba wa EFCC bisa yadda ta gudanar da gayyatar da ta taɓa yi masa sau biyu a lokacin da yake riƙe da mukaman gwamnati.
Ya ce hukumar ta nuna ƙwarewa da bin ƙa’idojinta a lokacin waɗannan gayyata.
A wani ɓangare na sanarwar, tsohon gwamnan ya jaddada cewa ya shafe sama da shekaru 11 tun bayan barin gwamnatin Kano, yana mai bayyana mukaman gwamnati da ya riƙe a tsawon rayuwarsa.
Ya ce ya yi shekaru takwas a matsayin gwamnan Kano, baya ga shekaru 17 da ya yi a aikin gwamnati.
Ya kuma bayyana cewa ya riƙe mukamin mataimakin shugaban majalisar wakilai a zamanin Jamhuriyya ta Uku.
Sauran mukaman da ya ce ya riƙe sun haɗa da wakilcin Arewa maso Yamma a Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Ministan Tsaro, mai ba shugaban ƙasa shawara kan batun Darfur da kuma Sanata a majalisar dattawa ta takwas.
Kwankwaso ya ce a tsawon waɗannan shekaru ya ci gaba da kiyaye mutuncinsa ba tare da wani tabo ba.
A ƙarshe, ya shawarci matasa da masu riƙe da mukaman gwamnati da su yi taka-tsantsan wajen mu’amalarsu da jama’a, yana mai tunatar da su cewa mulki ba na dindindin ba ne.
Ya ce: “Ku tuna cewa mukaman gwamnati na wucin gadi ne; waɗanda ke zaune a gidajen gilashi su yi hattara da jifan wasu da duwatsu.”
Ya kuma gode wa mutanen da ya ce ba su yarda da abin da ya kira yunƙurin yaudararsu ba, musamman waɗanda suka fito fili wajen kare mutuncinsa da tarihin ayyukansa.
