Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), ya soki sanya shugaban Hukumar Tara Haraji ta kasa (NRS), Zacch Adedeji, da Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, Taminu Yakubu, cikin kwamitin yakin neman zaɓen APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A ranar Asabar ne jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana sunayen mambobi 108 na kwamitin yakin neman zaɓenta na Shugaba Bola Tinubu domin neman wa’adi na biyu.
Jam’iyyar ta naɗa Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai kasance sakatare.
Haka kuma, APC ta naɗa Taminu Yakubu a matsayin ma’aji na kwamitin, yayin da Zacch Adedeji aka naɗa mataimakin daraktan tara kuɗaɗen yakin neman zaɓe.
A wata sanarwa da Kwankwaso ya fitar ranar Lahadi, ya ce sanya jami’an biyu cikin kwamitin yakin neman zaɓen jam’iyyar na iya zubar da mutuncin hukumomin da suke jagoranta.
Kwankwaso ya ce yadda aka tsara kwamitin yakin neman zaɓen APC ya kamata ya zama abin damuwa ga “dukkan ’yan Najeriya masu kishin ƙasa”, musamman a lokacin da farashin abinci da sauran abubuwan buƙata ke ƙaruwa.
Ya ce matasan Najeriya na fuskantar rashin aikin yi da raguwar damar samun abin dogaro da kai, yayin da manoma da ’yan kasuwa ke fama da matsalolin rayuwa.
Ya kuma ce miliyoyin ’yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro, yayin da bangarorin ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyukan gwamnati ke cikin matsin lamba.
Kwankwaso ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da abin da ya kira “cigaba da danniya”, tare da shugabanci da bai mayar da hankali kan jin daɗin jama’a ba.
