Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Jihar Kano, KCPC, ta samu izinin kotu domin lalata wani takin ruwa na miliyoyin naira da wa’adin amfani da shi ya ƙare, wanda ake zargin an yi yunƙurin sauya masa mazubi domin sake sayar da shi a kasuwa.
Hukumar ta bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarinta na hana yaɗuwar kayayyakin da suka lalace ko wa’adin amfani da su ya ƙare a kasuwannin jihar.
Sakataren zartarwar hukumar, Dakta Ibrahim Garba Muhammad, ya ce KCPC na ci gaba da ɗaukar matakai domin kare al’umma daga kayayyakin da ba su dace da amfani ba, waɗanda ka iya haifar da illa.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani ɗan kasuwa da suke zargin yana sayar da kayayyakin da suka lalace ko wa’adinsu ya ƙare, domin bai wa hukumar damar ɗaukar matakin da ya dace.
Dakta Ibrahim ya gargaɗi ‘yan kasuwa, kamfanoni da masu manyan shaguna da su kiyaye dokokin hukumar, tare da tabbatar da cewa kayayyakin da suke sayarwa sun cika ƙa’idojin inganci.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ke ƙarfafa sa ido kan kayayyakin da ake shigarwa kasuwannin Kano domin kare haƙƙin masu sayayya.
