Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta bukaci hukumar dakile da kula da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) da ta samar da karin alluran rigakafin cutar mashako domin karfafa yaki da cutar da kuma dakile yaduwarta a fadin jihar.
Bukatar ta fito ne yayin ziyarar Shugaban hukumar ta kasa Dakta Jide Idris nan Kano, inda ya tattauna da Kwamishinan Lafiya na Jihar Dakta Abubakar Labaran Yusuf kan matakan karfafa shirin tunkarar barkewar cututtuka, musamman Mashako da kuma yiwuwar bullar cutar Ebola.
A yayin ganawar, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bukaci a samar da karin alluran rigakafin Mashako domin tabbatar da cewa an kai su ga dukkan sassan jihar.
Da yake mayar da martani,Dakta Jide Idris, ya yi alkwarin tuntubar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta kasa (NPHCDA) domin samar da karin alluran rigakafin, kuma NCDC za ta sake duba tallafin da take bayarwa ta karkashin Asusun Tallafa wa Kiwon Lafiya na Matakin Farko (BHCPF) domin kara karfafa ayyukan kiwon lafiya a Kano.
Haka kuma, ya bukaci gwamnatin jihar ta samar da nata gudummawar kudi domin karfafa shirye-shiryen kariya da tunkarar cutar Ebola, yana mai jaddada cewa Kano na daga cikin jihohin da ke da matukar muhimmanci wajen shirin kariya daga cutar saboda filin jirgin saman kasa da kasa da take da shi da kuma matsayinta a Najeriya.
