
Ishaq Sani Dambazau
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya ba gwamnatin tarayya shawarar ƙaƙaba haraji kan kayayyakin man fetur da kuma ayyukan sadarwa domin ƙara kuɗaɗen shiga na gwamnati.
Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton IMF na nazarin tattalin arzikin Nijeriya na shekarar 2026, inda asusun ya ce ƙarin matakan haraji za su taimaka wajen samar da kuɗaɗen ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen tallafawa al’umma.
