Kasar Iran ta zargi Amurka da hana wasu muhimman jami’an tawagar ƙwallon ƙafarta shiga ƙasar, bayan ta amincewa ‘yan wasan da wasu ma’aikatan tawagar bizar halartar Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Kafar yada labarai ta Bbc ta rawaito Iran ta ce anƙi baiwa da dama daga cikin jami’an gudanarwa da masu bada shawara biza, lamarin da ofishin jakadancinta da ke Turkiyya ya bayyana a matsayin tsoma baki a harkokin wasanni saboda dalilai na siyasa.
Sai dai Amurka ta ce ta baiwa ‘yan wasan da ma’aikatan da ake buƙata biza, tare da jaddada cewa ba zata bari ayi amfani da tsarin gasar wajen shigar da mutanen da ake zargi da alaƙa da ta’addanci ba.
Iran ta kuma yi kira ga FIFA da ta shiga cikin lamarin, yayin da rahotanni daga Iran suka ce shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar da mataimakinsa na cikin waɗanda aka hana shiga Amurka.
A makon nan, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce ba za a amince da mutanen da ke da alaƙa da dakarun IRGC su shiga cikin tawagar ƙwallon ƙafar Iran ba.
