Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun su da laifin kai harin ta’addanci a cocin St. Francis Catholic Church da ke garin Owo, Jihar Ondo.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin bayan samun mutanen da laifuffuka tara, wanda suka hada da garkuwa da mutane, tallafa wa ayyukan ta’addanci da kuma amfani da abubuwan fashewa da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu.
Wadanda aka yankewa hukuncin sun hada da Idris Abdulmalik Omeiza, Al-Qasim Idris, Jamiu Abdulmalik da Abdulhaleem Idris.
Sai dai kotun ta wanke mutum na biyar, Momoh Otuho Abubakar, bayan ta bayyana cewa babu isassun hujjojin da suka danganta shi da harin.
Baya ga hukuncin kisa, kotun ta kuma yanke musu hukuncin daurin rai da rai kan kasancewar su mambobin kungiyar ta’addanci, tare da karin shekaru 20 a gidan yari kan laifin hada baki wajen aikata laifukan.
Harin da aka kai cocin a lokacin ibadar ranar Lahadi 5 ga Yunin 2022, ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan masu ibada tare da jikkata mutane da dama, lamarin da ya girgiza Najeriya da ma duniya baki daya. An dauki harin a matsayin daya daga cikin munanan hare-haren da aka taba kai wa wurin ibada a Najeriya.
