Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ce za ta ci gaba da yin sabbin naɗe-naɗe tare da kafa kwamitocin yaƙin neman zaɓe, yayin da take ƙara shirye-shiryenta domin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta bayyana cewa jerin sunayen jami’an da aka fitar zuwa yanzu mataki ne na farko, inda za a sanar da ƙarin muƙamai da kwamitocin gudanarwa a nan gaba.
A cikin wata sanarwa da mai ba ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, shawara kan yaɗa labarai, Phrank Shuaibu, ya fitar, ADC ta ce za ta kafa tsarin kwamitoci tun daga shiyya, jiha da ƙananan hukumomi har zuwa unguwanni da rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar.
Jam’iyyar ta ce za ta haɗa magoya baya, ƙwararru, shugabanni da matasa domin gudanar da ayyukan siyasa da kuma tsara manufofin da za ta gabatar wa al’umma.
Daga cikin batutuwan da jam’iyyar ta ce za ta mayar da hankali a kai akwai tsadar rayuwa, samar da abinci, noma, tsaro, ayyukan yi, masana’antu, ilimi, lafiya da bunƙasa tattalin arziki.
ADC ta ce manufarta ita ce samar da hanyoyin magance matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta tare da gina tsarin da zai shafi al’umma tun daga matakin ƙasa har zuwa rumfar zaɓe.